Home » Kurajen Zafi (Prickly Heat)

Kurajen Zafi (Prickly Heat), Kuraje ne da suke Fesowa Sakamakon Tsananin Yanayi na Zafi. Wannan Kurajen kan fesowa yara ko manya.

Wasu daga cikin kurajen na Sanya tsananin kaikayi. Akwai masu ruwa cikin su wanda ba sa kaikayi ko ciwo. Idan aka samu yanayi na sanyi, yawancin kurajen na bacewa sai dai wadan da suka tsananta.

A yawancin lokuta, Alamomin Kurajen zafin a manya na fesowa a wuraren da ke da matsi kamar wuya. Ga yara kanana kurajen sunfi fesowa a wuya, kirji, da kafada. Wani lokacin suna fesowa a Hammata Dantse ko Mazaunai.

Akwai wani nau`i na kurajen zafi wanda ke yawan fitowa daga Kasan Gashi. Anfi samun sa a wuraren da ke da gashi a jiki kamar Hammata, Ga’ba, Kai da sauran su. Ana banbanta kurajen zafi ne bisa ga yanayin tsanantar su a jikin fatar.

Babban Abin da ke haifar da Kurajen Zafi (Prickly Heat) shine toshewar hanyoyin fitan zufa a jiki. Idan suka toshe, A madadin  zufa ya fita sai ya tare a karkashin fatar mutum. Wannan ke Sanya kurajen da kuma Kaikayi.

Hadarin samun kurajen zafi na ‘Karuwa ga jarirai wadanda fatar su bata da kwarin fitar da gumi. Kasancewa cikin yanayi ko wuri mai Tsananin Zafi, Aikin ‘Karfi, Zazzabi, da yawan Kwanciya.

Kurajen zafi na warkewa a lokacin da aka samu canjin yanayi zuwa mai sanyi. Sai dai sukan tsananta musamman ga bakaken fata sabaoda ta kan sa su kara duhu. Ta kan Sanya tsananin kaikayi a wasu lokutan.

Domin kare kai daga kurajen zafi, kada a kunshe jarirai cikin kayan da babu iska. Sannan a Sanya kaya mara matsi kuma mai laushi ga manya. A zauna a wurin da ke da iska a lokacin zafi. Sannan a guji yawan aikin karfi. Kwanciya a wurin da ke da iska na da matukar anfani. Mayuka da ababen shafawa masu danko na da hadari a wannan yanayi, a guje su. Kare kai daga magunguna masu Sanya yin zufa na da muhimmanci domin kariya daga kurajen zafi.

Yabintu Abubakar

View all posts

1 comment

Leave a Reply