Home » Kulawa Da Lafiya A Islam

Kulawa Da Lafiya a Mahangar Addini, Wani Rukuni Na Ibada Wanda Allah Ta’ala Ke Azurta Bawa da shi. Amma kuma yakan jarabci bawa da akasin ta ko kishiyarta. Sannan ba`a hallaci bawa domin ya dawwama cikin koshin lafiya ba.

Masana sun bayyana cewa Lafiya tana daga cikin abubuwanda sharia ta tabbatar da cewa wani lokaci mutum zai rasa su.

Kamar Ita Lafiya, akwai wasu abubuwan guda bakwai wadan’da mutum zai fuskanci  kishiyoyin su a wani lokaci.

Cikin su akwai lafiya da kuma rashin lafiya.

A wasu lokutan mutane kan zama cikin koshin lafiya mai yalwa. Hakan ke sa a manta ma da cewar akwai rashin lafiya.

Wani lokacin kuma, wasu kan yi rashin lafiya na dogon lokaci da zai sa a manta da lokutan da suke da lafiya.

Akwai gwargwadon abin da Allah ta’ala yaso ya jarrabi dan Adam da shi kamar lafiya ko shain lafiyar, domin ko wannen su Jarabawace ta Allah.

Malamai sun bayyana cewa, rashin lafiya na zama kaffara ga mutum.

Sannan ba kasawa bace ko nakasu daga bangaren dan adam.

Rashin samun ingantacciyar lafiya a wani lokacin kan samo asali ne a dalilin sakacin mutum. Ko kuma kawai jarabawace daga Allah wanda duk kulawa da mutum ke da shi zai iya samun sa.

A bangaren kiwon lafiya ko neman Magani. Ba wayewa bace ko ibada mutum yace ba zai nemi managin wani larura da ke damun sa ba. Saboda masana sun bayyana cewa ba ita ce sunnah ta shari’a ko ta rayuwa ba.

Akwai Hadisai da dama da sukayi bayani kan kiwon lafiya a addini. wadanda ke nuni da cewa neman magani Sunnah Ce ta shari`a. Akwai bayanin kan ko wani cuta na da magani sai dai in ba`a gano shi ba. Don haka neman magani wajibi ne ga mara lafiya. Kamar Yadda Shehin Malami Ibrahim Sirajo PhD. (Dr Adhama) Yayi Wa Kafar Watsa Labarai Ta Waraka Media Concepts Bayani Cikin Wata Ganawa.

Yabintu Abubakar

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos