Home » Kin Yin Tsuguno A Lokacin Da Bahaya Ya Taso Yana  Kawo Cutar Basir

Kin yin tsuguno da wuri yayin da bahaya ya taso yana  kawo cutar basir.

Rashin shan ruwa akai akai da rashin amfani da Yar yarn itace ko ganyayyaki, da cin Abu Mai dusar fever, Basu kadai ke hadasa cutar basir.

Dabi’ar yin buris ko yin watsi da yin bayan gida a daidai lokacin da aka ji shi tare da jinkirta shi zuwa wani lokaci.

Wannan ɗabi’a tana sa bayan gida ya ƙara yin tauri sosai wanda hakan ke ƙara wahalar yunƙuri yayin yin bayan gidan. Wahalar yunƙuri fiye da ƙima yana takura jijiyoyin jini a cikin dubura har jijiyoyin jinin su kumbura.

Dalilin da ke sa bayan gidan ya ƙara tauri yana da alaƙa da tsawaitar zamansa a cikin babban hanji ko dubura fiye da yadda aikin jiki ya tsara. A wannan lokaci babban hanji yana ƙara tsotse ruwan da ke cikin bayan gidan yanayin da ke sa bayan gidan ya ƙara tauri.

Basir wanda ake kira da “piles” a turance, larura ce da ke ci gaba da shan gurguwar fahimta a tsakanin al’umma.

Mata masu juna biyu, kaso 50 na mata masu juna biyu na kamuwa da ciwan basir yayin goyan Ciki. Yawan shekaru musamman Wanda suka wuce shikaru 50. Tiba rukunin mutane masu jiki sosai sukan fada hadarin kamuwa da cutar basir.Ciye ciyen abinci barkatai wadanda ba Dusar feber a ciki kamar cake yougurt da sauransu

Nura Umar

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos