Home ยป KARIYA DAGA CIWON HAWAN JINI

Kariya Daga Ciwon Hawan Jini na da Muhimmanci sosai. Ciwon hawan jini wanda ake kira da BP, ciwo ne da ya yawai ta cikin al`umma. Hawan jini kan haifar da matsanantar cututtukan zuciya da ma shanyewar barin jiki idan ba`a magance shi ba.

Babban hanyar magance wannan ciwo shine ta hanyar Abincin da muke ci da kuma abin da muke sha. Wannan bincike ya gano nau`ukan kayan sha da ke da anfani wajen kawar da ciwon hawan jini da kuma wadanda ke tunzura shi.

BITRUT; Da farko dai nau`ukan abin sha da kan taimaka wajen rage hawan jini sun hada da lemon bitrut. Shi Bitrut na kunshe da sinadarin Naitret wanda ke taimakawa wajen sake hanyoyin jini. Wannan zai taimaka jinin jiki ya gudana yadda ya kamata. Masana sun bayyana cewa shan lemon bitrut na saukar da jini cikin awanni da shan shi.

BITRUT
BITRUT

ZOBO; Na biyu cikin jerin lemukan masu anfani shine lemon Zobo. Zobo na dauke da kaso mafi girma na abubuwan da ke inganta garkuwar jiki. Sannan kuma lemon Zobon na dauke da sinadarai da ake anfani da su wajen sarrafa magungunan rage hawan jini. Shan wannan lemo zai taimaka sosai wajen magance ciwon hawan jinin.

ZOBO
ZOBO

RUMAN; Lemon Ruman shima yana daga cikin yayan itatuwa da ke dauke da sinadaran da ke taimakawa wajen buda hanyoyin jini. Kamar lemon bitrut, shima yana taimakawa wajen inganta gudanar jinin jiki da kuma rage hawan jinin. An bayyana cewa shan akalla kofi guda na wannan lemon a rana zai taimaka wa masu ciwon hawan jini sosai.

ROMAN
RUMAN

RUWA; ruwa na da anfani mafi girma cikin jikin dan adam, ruwa na taimakawa wajen inganta lafiyar mutum baki daya. Shan ruwa na taimakawa wajen gudanar jini a jikin dan adam yadda ya dace ya kuma rage bugun zuciya. Har ila yau, ruwa na wanke hanyoyin jini da saukaka gudanan su cikin hanyoyin jinin.

RUWA
RUWA

A wani bangaren, akwai wasu ababen sha da ke tunzura ciwon hawan jini. Yana da muhimmanci a takaita shan su ko ma a kaurace wa shan su baki daya. Duk da cewa wasu binciken sun bayyana shan wadannan ababen sha a kaiyyade na taimaka wa lafiyar zuciya, babban abin da yake a fili shine illar su tafi anfanin yawa.

SHAYI; Ababen sha Masu dauke da sinadarin kafin kamar su shayin kowfi, ko bakin ganyan shayi. Illolin wadannan sun banban ta cikin mutane, yakan zama damuwa sasai yayin da wasu suka sha shi. Ga mai ciwon hawan jini kuma, ya kamata su guji shan wadannan shayin domin lafiyar zukatan su.

SUGA; Lemukan da ke dauke da Karin suga. Irin Su Lemukan kwalba ko roba masu gas da kuma Karin suga hadari ne ga masu ciwon hawan jinni. Yawan shan suga kan Sanya tarin kitse cikin jiki ya haifar da mummunan kiba. Sannan wannan zai iya zama tushen toshewar hanyoyin jinin jikin dan adam. Har ila yau yawan shan irin wadannan lemukan na Sanya Karin bugun zuciya da kuma hawan jini.

Abin lura anan shine, a kullum yana da muhimmanci mu kula da abinda muke ci ko sha. sannan, mu kasance masu son abin da jikin mu ke so domin lafiyar mu.

Kada mu manta, shan giya barasa hadari ne ga ilahirin lafiyan jiki baki daya. Sannan mu kula da sauran abubuwan da ke taimakawa lafiyar mu kamar motsa jiki, samun bacci yadda ya dace da kuma kaurakewa shan magunguna barkatai.

Tuntubar likitoci nada anfani a duk lokacin da muke son canza cimakan mu domin samun shawarwarin da ya dace. Wannan zai taimaka wajen rage kuskure wajen tsananta wata cutar, ta hanyar abinci ko sha ba tare da sani ba.

 

Yabintu Abubakar

View all posts

1 comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos