Home ยป `Karin Mahaifa (Fibroids)

`Karin Mahaifa (Fibroids) Wani Tsiro ne Dake Fitowa a Cikin Mahaifar Mace. Wannan Tsiron ba Cutar Daji bane. Sai Dai ya kan Girma Sosai Fiye Da Kima.

Kaso Daya Cikin Mata Biyar a Fadin Duniya na fama da wannan larura Ta `Karin Mahaifa a Shekarun su na Haihuwa. Sannan kuma Kaso Hamsin Cikin dari na Mata na Kamuwa da shi a Shekarun Tsufa. Ba`a Cika Samun shi Cikin Mata Masu Shekaru Kasa da Ashirin ba.

Ga Wasu Matan`Karin Baya Girma, Ciwo ko Damun su. Amma ga wasu, yana Girma kuma yana Haifar Da tsananin Damuwa a Garesu.

Lokacin da `Karin Mahaifa ya Kasance baya Ciwo, Bai Zama Lallai a Cire shi ba. Indai har Baya Girma ko damun mai Dauke da shi da Zubar Jini. Akan Gudanar da Aiki (Tiyata) Domin Cire `Karin Lokacin da aka samu wasu Alamomin na Damuwa.

Dukkan bincike a halin yanzu basu iya gano asalin Abubuwan da ke janyo kamuwa da `Karin Mahaifa ba. Sai dai ana hasashen cewa, ana iya gadon shi ko kuma Canjin Yanayin Jikin Mace kan Haifar da shi.

Girman `Karin Mahaifa bashi da iyaka. Sannan kuma yakan zama dan karami yadda idanu baza su iya ganin Shi ba sai da taimakon na`ura. sannan yakan Tsiro a Kowane Bangare na Mahaifar Mace.

Alamomin Cutar `Karin Mahaifa (Fibroids) sun hada da Zubar Jini a lokacin da ba na al`ada ba. Yawan zubar da Jini Fiye da Kima a lokacin al`ada, ko Wuce Kaiyadadden Kwanakin al`adar Mace. Jin Fitsari akai-akai, Ciwon Mara, Kumburi a Kasan Mara da Jin Zafi Yayin Jima`i. Dukkan wadannan na daga cikin Alamun da Mace ke samu yayin da ta Kamu da Cutar `Kabar Mahaifa.

Tsanantar Cutar kan Haifar da Matsalar Karancin Jini a Jiki. Cutar Mafitsara, Rashin Haihuwa, Yawan `Kaban a ciki Wanda zai Sanya Dole a Cire shi. Ya kan sa a Haifi Yaro Kafin Lokacin yayi Saboda Karancin Wurin Zama a Ciki. Ko Kuma Mace ta kasa Haihuwa a lokacin da Tsiron ya Rufe Hanyar Fitar abin da ke cikin ta. Sai dai ta Hanyar Tiyata.

Magance Wannan Cuta ya Danganta da Lafiyar Mutum, Shekaru da Alamomin Cutar. Haka zalika, yanayi na Juna Biyu ko Neman Haihuwa na Mara Lafiya kan Shafi Magance Cutar.

Likitoci na iya bada magunguna domin kawar da wasu daga cikin alamomin kamar Zubar Jini, Radadi, Magance Matsalar Karancin Jini da sauran su.

Akan iya gudanar da aiki domin cire `kaban daga cikin mahaifa. Samun Juna Biyu kan Kara Hadarin Girman `kaban ga mai dauke da ita. Hakan na faruwa ne saboda ‘Karuwar Gudanar Jini a Jiki. Ya kan Sanya Tsananin Zubar Jini ga Macen da ta Haihu.

 

Yabintu Abubakar

View all posts

1 comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos