Home ยป ILLAR SUGA GA YARA

Yawan Shan Suga ko Zaki Mai Yawa Cikin Abincin Yara na Haifar Musu da Matsananciyar Damuwa ga Lafiyar su.

Illolin Da Suga Ko Zaki Suke Haifarwa Da Yara Sun Hada Da;

RAGE GARKUWAN JIKI; wannan na nufin shan sugan yara kanana kan rage musu garkuwan jiki. wannan zai Sanya su saurin kamuwa da cututtuka musamman irin su Mura, Tari da Yoyon Hanci. Yana da anfani mu sauya shan zakin su kamar su Alawa, Biskit da Sauransu da `ya`yan Itatuwa. Sturoberi wanda zai taimaka wajen lafiyar Kwakwalwa, Ayaba Yana Taimaka Musu Wajen rage musu gajiya. Sannan irin su zuma da lafiyayyen biredi da ke da sinadarai da zasu taimaka wa girman yaro.

KIRINIYA; shan zaki na Sanya yara rashin mai da hankali kan abubuwan da ke da anfani. Yana kara musu tsoro da kuma kiriniya. Sannan yana hana yaro mai da hankali kan muhimman abubuwa. Basu abincin da ke kunshe da sinadarai kamar Fotashiyon na cikin Ayaba zai taimake su wajen mai da hankali da koyo.

RAGE KARFIN IDANU; yawan shan suga na rage wa yara karfin idanu su daina gani sosai. Rage sugan kan dawo da ganin su yadda yake. Cin irin su Kwai, Karas, Abokado, Brokoli da kifi zai taimaka wajen inganta gani, musamman ga yara kanana.

MATSALOLIN CIKI; lokacin da yaro ke shan zaki sosai irin su alawa ko lemon kwalba, su kan samu matsala a ciki. Wadannan matsalolin sun hada da kumburin ciki, rashin narkewar abinci a ciki, gudawa da sauran cututtukan ciki baki daya. Idan yaro na yawan fama da wadannan matsaloli ya kamata a canza abinci sa. Cin abinci irin su Dankalin Hausa, Ayaba, Yogot, Shinkafa da kunun hatsi na da anfani.

CUTAR SARKEWAR NUNFASHI (ASMA); Bincike ya alakanta yawan anfani da suga ga yara kanana da cutar Asma. Yawan sugan kan haifar da cuta ga hanyoyin nunfashin wanda zai sa yaran atishawa da ma sarkewar nunfashin. Idan yaro na fama da irin wannan larura yana da muhimmanci a sauya masa kayan zakin nan da `ya`yan itatuttuwa kamar Baure, da dangin sturoberi.

CIWON SUGA; ga yara kanana, shan zaki kan haifar musu da ciwon Suga. Shan suga mai yawa da jikin su bazai iya konawa ba kan haifar da matsala ga muhimman gabobin jikin su ta kuma Sanya su kamuwa da ciwon suga. Mu kare `ya`yan mu daga ciwon suga ta hanyar basu abincin da ya dace.

CIWON RANA NA YARA; yawan shan zaki musamman na `ya`yan itatuwa kan sa yara gudawa idan aka sha su dayawa. Duk da cewa `ya`yan itatuwa na da anfani ga jikin yaro, yana da muhimmanci mu lura da adadin da yara zasu sha a rana.

KARANCIN FAHIMTA; ga yaran da ke shan suga, yanayin fahimar su na raguwa. Sugan na shafar barin kwakwalwar yaro ya Sanya su zamo marasa fahimta sosai. Idan yaro bashi da kokari a makaranta a kula da shan zakin sa a rage.

KYASBI NA YARA; yawan anfani da suga ga yara na haifar musu da cutar fata ta kyasbi. Suga na kara sinadarin Insulin a jiki, saannan ya sa cuta a fatar. A lokacin da aka kula da fatar yaro ya soma canzawa, a sauya masa yawan zaki da man Kifi da kuma Ruwan lemun tsami kadan ko wani rana. Wannan zai magance matsalar ta fata.

CIWON HAKORI; lokacin da kwayoyin cutar Bakteria dake cikin baki suka cinye sugan, suna samar da sinadarin asit. Wannan asit din ke Sanya rubewa da kuma ramukan hakora. wannan kan sa matsanancin ciwon hakori.

Ga wasu yara, yawan shan zaki na sa sauye-sauye da dama a jikin su. Wannan wani lokacin ya na sa a kasa sanin takamaimai dalilin da ya Sanya hakan. Lokacin da aka ga yaro na kin cin wani nau`in a abinci, ko shiga wani yanayi da Zarar ya ci, to a kula da zakin ko kuma suga dake cikin abincin.

Yana da muhimmanci ga iyaye su kula da abin da suke ci su kansu. A koda yaushe, yaro kan koyi dabiu da abubuwa daban-daban daga iyaye ko na sama da su. magance illar suga ga yara na da anfani wajen girma da lafiyayyun yara.

Shan Taba Sigari a Wurin Da Yake akwai Yara Yana da Matukar Hadari..

Yabintu Abubakar

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos