Home » Gyada (Groundnuts)

Gyada (Groundnuts) Abinci ne da ake Amfani da shi Duniya baki daya. Ana Amfani da ita wajen Sarrafa Mai Wato Man Gyada, Kuli-Kuli ko Karago, Markadaddiyar Gyada don yin Kunu da Sauran su. Wasu na iya Cin Danyar Gyada, Dafaffiya, Soyayyiya Da Kuma Gashashshiya. Sannan ana sanya ta a Miya ko wasu nau`i na abinci.

Dunbin Alfanu da Gyada ke da shi kan Sanya ayi Amfani da ita a kullum. Gyada tana Dauke da Muhimman Sinadarai Daban-Daban.

Gyada na Dauke da Sinadarin Bitamin, Minaral, Frotin, Amino Asit, da Kitse Mai Amfani do  yake kare Mutum Daga Kamuwa da Ciwon Zuciya, Ciwon Suga, Rage Kiba, Kara Kuzari da Bada Wadataccen Bacci. da Inganta Lafiyar Zuciya Baki Daya.

Wannan nau`in Abinci na da Sauki Sosai. Ana iya Samunta ko ina a fadin Duniya.

Gyada Bata da Sinadarin Cabohaidret Sosai a Cikin ta. Wannan ya Sanya ta Zamo Abinci mai Inganci ga Masu Ciwon Suga.

Har wa yau, Gyada na da Ingantaccen Sinadarin Frotin a Cikinta. Duk da Cewar Jikin Wasu baya karbar wannan Sinadarin. Gyada tana da Matukar Muhimmanci Wajen Gina Jiki da kuma Kara Kuzari.

Gyada tana kuma dauke da Sinadarin Bitamin da Minaral Masu Yawa. Irinsu Bitamin E, B1, B3, B9, Magnishiyom, Cofa, Posforos. Antiokzidant.

Muhimmancin Gyada ga lafiyar Jiki sun Hada da;

Kara Kaifin Basirar Kwakwalwa; Bincike ya nuna Cewar Yawan Amfani da Gyada (Groundnuts) ko da Cikin Tafin Hannu ne a rana na kara Kaifin Basira. Sannan Yana Kare Mutum Daga Cututtukan da suka Shafi Kwakwalwa Kamar Cutar Mantuwa. Sinadaran da ke ciki na Taimakawa Kwakwalwa Wajen Gudanar da Aikinta Yadda Yadace. Sannan kuma Tana Rage Damuwa da sa Bacci Domin Lafiyar Kwakwalwa.

Karin Kuzari da Karfin Mazakuta: Masana sun ce Sinadarin Nitrik Okzat Dake Cikin Gyada na Buda Hanyoyin Jinin Jikin Dan Adam. Sannan kuma Bincike ya Nuna Cewar Amfani da Gyada Kan Taimaka Wajen Magance Matsalar Mazakuta da Inganta Lafiyar Jima`i. Haka Zalika tana Taimakawa Mata da Maza Wajen Samun Wadataccen Ruwan Maniyi  da kuma Samar da Haihuwa ta Fannin Inganta Kwayoyin Halittar da Namiji.

Rage Kiba; Yawancin Abincin Dake Kara Kuzari na Taimakawa Wajen Rage Kiba. Gyada tana sa Koshi da Wuri da kuma Rashin Jin Yunwa. Wannan zai Taimaka Wajen Rage Yawan Cin Abinci da kuma Rage Kiba. Duk da Cewar Tana da Kitse, Wannan Kitsen baya sanya Kiba.

Ciwon Suga; Wannan Abinci Wato Gyada tana Rage Hadarin Kamuwa da Ciwon Suga. Abinci ne Mai Kyau ga Masu Ciwon Suga. Wannan Abincin na Taimakawa Wajen Rage Yawan Suga a Cikin Jini. Amfani da Gyada na Saurin Kosar da Mutum, Tatso Sinadarin Kalshiyom daga Cikin Abinci.

Cutar Daji; Muhimmamn Sinadaran Dake Cikin Gyada na Taimakawa Wajen Hana Kamuwa da Cutar Daji. Amfani da Gyada na Kare Kamuwa daga Cutar Dajin Mama na Shekarun Girma. Dajin Ciki da na Sauran Gabobi.

Zuciya: Gyada tana da Amfani Wajen Inganta Lafiyar Zuciya da Kuma Kare ta Daga Kamuwa da Cututtuka Saboda Muhimman Sinadarai da ke Cikinta.  Gyada tana Taimakawa Wajen Rage Sinadarin Kolestrol. Sannan kuma tana Kare Jijiyoyi da Hanyoyin Jini daga Cututtuka.

Fatar Jiki; Alfanun Gyada ya Hada da Kare Fatar Jiki daga Kunar Rana. Siandaran Bitamin, Zink, da Magnishiyom Dake Cikin Gyada  suna Yakar Kwayoyin Cuta na Bakteria a Jikin Fata da kuma Sanya Fatar Sheki. Bita Karotin Dake Cikin Gyada na inganta Fatar Jiki. Haka zalika Maikon Gyada yana Kare Fata Daga Yankwanewa, Tsufa,  Kyasbi, da Sauran Kuraje.

Gashi: Masana Sun Bayyana Cewar Dukkannin Sinadaran Dake Cikin Gyada Na da Muhimmanci Wajen Inganta Lafiyar Gashi. Wadannan suke Kare Gashi Daga Bushewa da Kuma Karyewa. Sannan kuma suna Taimakawa Girman Gashin Da kuma Laushi.

Amfani da Gyada (Groundnuts) Fiye da Kima a Rana Kan Haifar da Matsaloli da Dama a Jikin Mutum. Wani lokaci yakan Haifar da Matsalar Hanta Idan Amfanin Yayi Yawa. Musamman idan akayi anfani da Wadda Tafara Danshi ko Lalacewa.

Wadanda jikin su bai amshi Amfani da Gyada ba. Su kan Samu Yoyon Hanci, Mura ko Wani Ciwo na Daban. Yana da Muhimmanci su Tuntubi Likita a Lokacin da sukayi Amfani da Gyada Cikin Rashin Sani.

Amfani da Gyada da Yawa kan Sanya Cushewar Ciki da kuma Hana Jiki Tatsar Sauran siinadari Dake Cikin Abinci.

Yabintu Abubakar

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos