Dawa (Sorghum) na daga cikin Dangin Hatsi da suka samo asali daga nahiyar Afrika. Tarihi ya nuna cewar, mutanen wannan nahiyar ke noman ta. Sannan kuma tana daya daga cikin hatsi masu tarin anfani ga lafiyar jikin dan adam.
Ita Dawa na kunshe da muhimman Sinadarai masu matukar anfani ga lafiya. Wadannan sinadarai sun hada da Bitamin, Minaral, Faiba, Antiokzidant da sauransu. Faiba da ke cikin ta na taimakawa wajen narkar da abinci a ciki. Sannan tana da anfani wajen tatsar alfanu dake cikin abinci da mutum ya ci. Ta na kare kunburin ciki da sanya samun Bayangida cikin sauki.
Anfani da dawa na taimakawa masu fama da Ciwon Suga domin a hankali take bada nata sugan a cikin jini ta yadda ba zai cutar da mutum ba. Wannan ya sanya ta kasance lafiyayyen abinci ga masu wannan ciwo na Suga.
A Bangaren Lafiyar Zuciya, anfani da dawa na da muhimmanci wajen inganta Lafiyar Zuciya, Rage Sinadarin Kolesterol a cikin jiki, da kare dukkan Cututtukan da ke da alaka da zuciya. Ga dukkan masu bukatar ingantacciyar Lafiyar Zuciya, Sanya dawa cikin Abincin Yau da Kullum kan Taimaka.
Har ila yau, Dawa na dauke da sinadarin Antiokzidant dake taka muhimmiyar rawa wajen kawar da kwayoyin da ke sanya cututtuka cikin jikin mutum. Tana inganta garkuwan jiki baki daya.
Saboda tarin alfanu da Dawa ke da shi, tana da muhimmanci a sanya ta cikin abincin yau da kullum. Za`a iya sarrafa abubuwa da dama da dawa. Za`a iya Musanya Shinkafa da Dawa, Dambu ko Tuwo, Kus-Kus, Kunu da sauran su. Sauya flawa da Dawa wajen yin Cin-cin, fanke, dan-wake, waina, da sauran su zai bada ma`ana.
Dawa (Sorghum) na da anfani fiye da yawancin hatsi da muke anfani da shi. mu inganta lafiyar mu da sauya wasu daga cikin abincin mu da dawa.
Add comment