Home » Fitsarin Jini Wato Bilharzia

Fitsarin jini wato Bilharzia, cuta ce Wanda tsusan ciki ke kawo shi. Wannan cutar na shafar hanji da Kuma mafitsara.

Saboda kasancewar tsusan na bin jini tana iya shafar sauran sassan jikin Dan adam. Wadannna sassan sun hada da huhu, jijiyoyi da suma kwakwalwa.

Cutar fitsarin jini ba ta nuna alamu sosai daga kamuwa da ita. Amma yakan tsananta da dadewar ta a jikin Dan adam ta shafi dukkan jikin Dan adam.

A yara kanana cutar fitsarin jini kan Sanya rashin girma da Kuma matsalar kwakwalwa.

Wani lokacin cutar bilharzia ta kan kama tsuntsaye da sauran dabbobin gida.

Don haka, ana kamuwa da wannan cutar ta hanyar taammali da ruwan da ke dauke da tsutar Wanda idanu bata iya kallon su. Musamman Ma yayi iwo ko wanka.

Hakazalika iwo ko wanka,wanki da ruwan da ta gurbata da tsutar cutar na Kara hadarine kamuwa da ita.

Sannan shiga kwanceccan ruwan ko kuma wanke kayan abinci da ruwan da ke dauke da cutar ko Sha suma na sa a kamu ta cutar.

Yawanci dodon kodi ke yada wanna kwayoyin tsutar a cikin ruwan. Ko kuma idan Mai dauke da cutar yayi bahaya ko fitsari a cikin ruwan da ake anfani da ita.

Wannan cutar ta fitsarin jini na shafar sassan jikin kamar su mafitsara, huhu, hanta, kashin gadon baya, dama kwakwalwa.

Ba’a daukan wanna cutar daga mutum Kai tsaye. Sai dai cikin ruwan da ta gurbata da tsutar dake kawo cutar.

Cutar fitsarin jini na Bilharzia na iya kama manya da yara.

Wadanda ke da hadarine kamuwa da ita sun hada da masu Iwo, ko masu sanaar da ke da alaka da rafi ko tabki.

Yaran da ke wasa a kwancaccen ruwan sama na cikin hadarin kamuwa da cutar fitsarin jini.

Alamomin cutar fitsarin jini na Bilharzia na bayyana cikin makonni biyu da shigar tsutar zuwa watanni uku.

Sannan yakan bayya alamomin kamar fesowar kuraje, zazzabi, ciwon Kai, ciwon jiki da numfashi dakyar.

Sauran manyan alamomin sun hada da kumburin cikin, gudawa, bahaya Mai jini da  fitsarin jini.

Fitsari Mai zafi, dajin mafitsara, dajin hanta duk alamu ne na cutar

Likitoci sun bada shawar a garzaya asibiti a lokacin da wadannna alamomin ko wasu daga ciki suka bayyana.

Zaka iya kare wannan cutar ta hanyar kiyaye Kai daga iwo a kogi ko rafi, kiyaye shan ruwan rafi ko kogi, cin abincin da aka wanke da wannan ruwan, wanki ko wanka da ruwan.

Tafasa ruwan Sha da na anfanin gida musamman ga wadanda ke anfani da ruwan rafi ko kogi, dama na rijiya.

Wannan zai taimaka wajen kare kamuwa da cutar fitsarin jini.

Wannan cutar ta fitsarin jini wato Bilharzia, bata da rigakafi.

Saboda haka, ya dace abi sauran hanyoyin kariya daga wannan cutar.

Yabintu Abubakar

View all posts

1 comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos