Home ยป Cutar ‘Kabar Ciki (Hernia)

Ciwon Kabar Ciki (Hernia) na samuwa ne a lokacin da Hanjin Mutum ya shige Wani Bangare na Cikin Ciki ko Jijiyoyi. wannan yanayin kan Sanya Makalewar Hanjin. Wani sa`in wannan na Haifar da Ciwo Musamman a yayin da mutum ke Motsawa. Kamar Sunkuyawa, Tari ko Daukar abu mai Nauyi.

Kabar Ciki bata Cika Haifar da Matsala ba. Sai dai idan ta Tsananta, ta kan sa Tsananin Ciwo da kuma wasu Matsalolin Daban.

Alamomin wannan ciwo sun hada da Kumburin Gefen Mara, Kaikayi, Radadi Musamman Lokacin da Mutum ke Motsawa. Ciwo ko Mutuwar Gefen Marar Mutum a Lokacin da yake daga abu mai Nauyi. Idan Shigewar Hanjin ya Kasance ya sauka ta kasa, yakan Sanya Ciwo a ‘Ya’Yan Marainan ‘Da Namiji.

Ga Yara Kanana, Cutar tana Bayyana ne a lokacin da Jaririn ke Kuka, Tari, ko Yunkurin yin Bayangida. Ya kan Sanya su yawan kuka, Rashin Cin Abinci da Kuma Rashin Nutsuwa.

Ababen da ke nuna alamun damuwa ga wannan ciwon sune lokacin da Cutar ta Harde yadda zata Hana Jini Gudana a Jiki. Hakan kan Sanya Tashin Zuciya, Amai, Tsananin Ciwo, Canza lau`nin Fatar Wajen ko Rashin iya Bayangida ko Iska Wato Tusa.

Wasu lokutan babu wani takamaiman abin da ke haifar da wannan ciwo. Amma akan danganta shi da ababe kamar haka; Samun Damuwa a Karkashin Cibiya. Rashin Kwarin Naman Ciki, yawan yunkuri yayin Fitsari ko bayangida. Aikin Karfi, Juna Biyu ko Tari da Atishawa Mai Karfi. Yawanci ana Samun Sarkewar Naman Cikin tun daga Haihuwa. Amma akwai wasu abubuwan da ke kara hadarin kamuwa da wannan ciwon. Ciwon Kaban Ciki ( Hernia) yafi kama Maza, Kaso 80 na Maza bisa 20 na Mata. Shekaru, Farin Fata, Asalin Ciwo a Dangi, Yawan Tari, Shan Taba. Cutar Basir, Kumburin Hanji, Juna Biyu da Haihuwar Bakwaini na wasu daga cikin ababen da ke kara hadarin kamuwa da wannan ciwo.

Tsanantar ‘Kabar Ciki na Sanya Tsananin Ciwo a yankin ‘Kabar. Ga Maza tana iya shiga Maraina Idan Har ba`a Magance shi ta hanyar Gudanar da Aiki Wato Tiyata.

Hanyoyin Kariya daga wannan ciwon sun hada da cin ingantattun abinci domin hana yawan yunkuri yayin bayangida. Cin abinci masu dauke da sinadarin faiba, `ya`yan itatuwa da ganyayyaki. A guji daukan abu masu Nauyi Sosai ko kula da yadda ake daukan Nauyin. Sannan A daina shan Taba.

Yabintu Abubakar

View all posts

1 comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos