Home ยป CUTAR AMOSANIN JINI

Cutar Amosanin Jini wanda aka fi sani da Sikla, Tana daya daga cikin Cutar da ake gadon ta daga iyaye. Wannan ciwo na shafar barin jinin jikin mutum da ke raba sinadarin Oksijin Ga sauran sassan jiki.

Yanayin kwayoyin jinin dan adam yana Kasancewa ne a dunkule, amma ga masu wannan cuta Abun Ya Sha ban-ban, jinin yakan kasance kamar lauje. Hakan Kan Sanya jinin baya gudana yadda Yakamata.

Akasarin masu dauke da wannan ciwo kan fara samun alamomin Cutar a lokacin da suka kai watanni shida da haihuwa. Alamomin kan banbanta cikin mutane. Sai dai yawancin su na nuna alamomin kamar haka;

KARANCIN JINI; Ga mai lafiya, kwayoyin jini kan kai kimanin kwanaki dari da ashirin kafin wasu su maye gurbin su. Jinin Mai dauke da ciwon Amosani na mutuwa cikin kwanaki Goma zuwa Ashirin wanda hakan kan bar gibi kafin cikar sauran kwanakin. Wannan yakan sa su samu karancin jini a jiki wanda kan haifar da tsananin gajiya a jikin su.

TSANANIN RADADI; masu wannan ciwo na yawan fama da tsananin radadi a yawancin lokuta. A yayin da kwayar jini mai kama da laujen ya toshe wata hanyar jini, saboda yunkurin wucewa da jinin ke yi, akan samu tsananin radadi a gabobi da dama. Ga wasu mutane, wannan kan dau awanni zuwa kwanaki ko satuka. Ta kan Sanya a kwantar da su a asibiti a wasu lokutan.

Wasu daga cikin masu dauke da wannan ciwo na fama da tsananin radadi sakamakon samun matsala ta kashi da gabobi.

KUMBURIN KAFAFUWA DA HANNAYE; toshewar hanyoyin jinin kan haifar da kumburi a kafa ko hannun mai dauke da ciwon.

SAURIN KAMUWA DA WASU CUTUTTUKA; Masu dauke da Sikla na saurin kamuwa da wasu cututtukan sakamakon gurbacewar garkuwan jikin su. Yawanci akan bawa yara magungunan da rigakafi da zai kare su daga wasu cututtukan da kuma inganta garkuwan jikin su.

RASHIN GIRMA KAN LOKACI; yawancin masu dauke da Amosanin jini basa girma kamar sauran yara a lokacin da ya dace. Wannan ciwo na mai da su baya ta fannin girma.

MATSALAR IDANU; Lokacin da kwayoyin jini na Sikla mai kama da laujen ya toshe wata hanya ta jini ta fannin idanu, yakan haifar da matsala ga idanun ko ma rashin gani baki daya.

Ana kamuwa da wannan ciwo ne a lokacin da iyaye biyu ke dauke da kwayoyin jini na Sikla. Idan ya kasance daya daga cikin suke dauke da shi, yaro zai iya gada. Zai kasance yana da shi a jiki amma mara tasiri. Ba za ta numa alamu ba sai dai in ya girma shima zai iya gadar wa yayan sa.

Ba`a samun wannan ciwo ta wani hanya daban bayan wannan. A koda yaushe, iyaye ke gadar da shi ga yaya.

Ciwon Amosanin Jini wato Sikla idan ya yi tsanani ya kan haifar da wasu cututtukan daban. Wadannan cututtukan sun hada da shanyewar wani Bangaren Jiki ko Rashin iya anfani da wani sassa na jiki kamar Baki, Hannu da Kafa. Ciwon zuciya Sakamakon Toshewar Hanyoyin Jini da Rashin Kwarin Kashi. Haka zalika, suna yawan kamuwa da Ciwon Hawan Jini, lalata wani bari na jiki kamar Hanta, Huhu, da Koda. Wannan Ciwo na Janyo Matsala ga mai Juna Biyu, Rashin Haihuwa ga Maza, Rashin Karfin Muamala ta Aure, Ciwon Makanta da Ciwon Kafa.

Haka zalika ya kan sanya Kumburin Saifaa harma ta kai ga fashewa idan tayi tsanani. wannan kan sanya a rasa rai baki daya.

Kariya ga wannan ciwo ya hada da sanin lafiyar jini ga wadanda zasu yi aure don gudun hada masu dauke da kwayoyin biyu. Masu dauke da kwayoyin biyu ne kadai zasu haifi mai ciwon.

Tuntubar likita a lokacin da masu dauke da kwayoyin ke bukatar haihuwa don gwaji da shawarwarin yadda zasu kauce wa haifar mai ciwon.

Yabintu Abubakar

View all posts

2 comments

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos