Home ยป Ciwon Olcer

Hukumar yaki da cutttuka masu yaduwa NCD reshen jahar Kano ta bayyana cewa sama da mutane dubu daya #1000 ke kamuwa da cutar olcer, saidai abin takaicin shine haryanxu akwai dubun dubatar mutanen daba su san suna dauke da cutarba.


Baya ga kwayoyin cutar ,wani abu dake haifar da olser shine Shan magunguna ba bisa ka idaba, daya ke tsokaci mataimakin daraktan kula da lafiyar alumma dakuma cututtuka masu yaduwa a ma’aikatar lafiya ta jahar Kano Dr ibrahim aliyu Umar yace gwamnati na kokari ta fadada aiyyukanta na kiwon lafiya yankunan jahar nan, tare da bada ishasshiyar kulawa gamasu fama da cutar olser.


Yace a kowacce rana a hajar Kano a kalla ana samun mutane dubunnai wadanda suke da wannan cuta ta olser , yace shiyasa a tsarin bada magani da ake dashi gwamnati tayi amfani dashi trouble bundle founds, aka saka magungunanan olser din Wanda zasu taimakawa marasa lafiya ya samu magani Mai kyau, Mai inganci kuma yasameshi cikin sauki.


Haka kuma Dr ibrahim yakara dacewa yawan Ciwon kirji, yawan cushewar ciki, dayawan yin amai dakuma Ciwon ciki da dai sauransu sune wasu daga cikin Alamomin cutar olser.


Ya kuma bukaci alumma dasu garzaya cibiyoyin lafiya Mafi kusa dasu domin daukar matakin gaggawa idan har mutum yaji wadannan alamu.


Yawanci idan mutum yaji cikinsa babu dadi ko Yana yawan gyatsa ko yawan yin hutu (wato tusa) kokuma mutum Yana Jin zafin kirji ko soyewa a cikin kirjinsa kowani Abu makamancin haka to mutum ya garzaya asibiti sannan kuma ya sha magani da wuri.


Ita dai wannan cuta ta olser idan ba asha magani da wuriba Tana iya Huda ciki ko hanji Wanda idan hakan yafaru mutum zai iya samun Ciwon ciki ko kunburun ciki ko mutum yafita daga haiyyacinsa daga nan mutum ka iya rasa ransa baki daya.


Manufar cigaba Mai dorewa ta majalisar dinkin duniya SDG3 ita ce jaddada bukatar tabbatar da lafiyar al’umma Nan da zuwa shekara ta 2030.

Dan haka zuwa asibiti akan lokaci domin gano cuta dakuma dakatar da yaduwarta nada matukar muhimmanci domin samun koshin lafiya Mai dorewa.

Suwaiba Abdullahi Sarki

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos