Home » Cimaka Ga Sassan Jiki Daban-daban

Abu ne da yake da matukar muhimmanci mu san nau’ikan cimaka da kowanne sashin jiki ke bukata domin gudanar da ayyukansa yadda ya kamata.

Hakan ne yasa muka zakulo muku jerin jadawalin abincika da sassan jiki daban-daban ke bukata wajen aiwatar da ayyukan su yadda ya kamata.

NA FARKO, KWAKWALWA
Me ya kamata na dinga chi domin inganta ayyukan kwakwalwa?
Daga cikin abubuwan dake inganta ayyukan kwakwalwa akwai Blueberries, kifi, dangogin su gyada, chakuleti da sauransu.

Wadannan dangogin cimaka na samar da sinadaran ANTIOXIDANTS da OMEGA-3, wadanda su kuma ke taimakawa wajen inganta ayyukan kwakwalwa na kaifin tunani da saurin fahimta.

NA BIYU, ZUCIYA
Ana bukatar mutum ya dinga chin wadannan nau’ikan abincika domin inganta Lafiyar zuciyarsa ta yadda zata gudanar da ayyukan ta yadda ya kamata. Daga cikinsu akwai ganyayyaki musamman ma korayen ganyayyaki, kifi, dangogin su kayan tsaba irinsu gero da dangogin su gyada (wanda suka hada da Aya da dai sauransu).
Wadannan nau’ikan cimaka na kunshe da muhimman sinadarai dake taimakawa ayyukan zuciya da kare ta daga hadarukan ciwukan zuciya.

NA UKU, FATAR JIKI
Fatar jiki na bukatar nau’ikan abincika irinsu Avocado,Tumatir, Dankalin turawa, dangogin su gyada, koren shayi da sauransu domin inganta lafiyar fata.

Wadannan nau’ikan cimaka cike suke da sinadaran Vitamins daban-daban hadi da kuma ANTIOXIDANTS wanda su kuma ke sanya fatar tayi kyau tare da kareta daga lalacewa, haka kuma wadannan sinadaran na taimakawa matuka wajen kiyaye lafiyar fatar.

NA HUDU, KASHI
Daga cikin nau’ikan cimaka dake taimakawa lafiyar kashin mutum sun hada da Madara, Cheese, ganyayyaki musamman koraye.
Wadannan nau’ikan cimaka na dauke da sinadarai irinsu CALCIUM, VITAMIN D da wasu daga cikin MINERALS wadanda keda matukar muhimmanci ga lafiyar kashi hadi da kwarinsa.

NA BIYAR, GARKUWAR JIKI
Garkuwar jikin dan adam ita kanta akwai nau’ikan cimaka dake taimaka mata wajen inganta ayyukan ta na yaki da hare-haren cututtuka. Daga cikin wadannan cimaka akwai dangogin Y’ay’an itatuwa masu kaifi a harshe irinsu lemon tsami, tafarnuwa, citta, hadi da nau’ikan YOGURTS da dai sauransu.

Wadannan abincika na dauke da sinadaran VITAMINS da ANTIOXIDANT, wanda ke tallafawa wajen karfafa garkuwar jikin wajen yakar cututtuka.

Mu inganta ayyukan sassan jikkunan mu ta hanyar wadata su da nau’ikan abincika da suke bukata.

Umar Abubakar Imam

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos