Home » Ayaba (Banana)

Ayaba (Banana) na Daya daga Cikin YaYan itatuwa da ake Nomawa, Sayarwa da Kuma Ci a duk Fadin Duniya. Sannan kuma tana da Yanayi Daban-Daban Sama da Dubu Daya bisa ga Bayanin Kungiyar Manoma ta Duniya  (FAO).

Ayaba na da Muhimman Sinadarai da Suka Hada da Fotashiyon, Mineral, Faiba da kuma Bitamin. Wadannan Sinadaran na Taimakawa Wajen Inganta Lafiyar Al`umma da kuma Kariya Daga Cututtuka da Dama.

Ayaba na daga Cikin Ababe da ke Yaki da Cututtukan Zuciya, Ciwon Suga da Magance Matsalar Raunin ‘Kashi.

Alfanun Ayaba a Jikin Dan Adam na da Matukar Yawa. Sannan Ayabar Magani ce ga abubuwa da dama a Jiki.

Na Farko Ayaba na rage Mummunan Kitse a Cikin Jikin Mutum Saboda Tana da Sinadarin Faiba. Tana Taimakawa Wajen Tatsar Abincin da Mutum ya ci Yadda yadace.

Sinadarin Fotashiyon dake cikin ta na Taimakawa Wajen Magance Matsalar Hawan Jini. Wannan Sinadarin na Taimakawa Jiki Fitar da Sinadarin Sodiyom da yayi yawa a Jiki ta Cikin Fitsari. Haka zalika, tana sake Hanyoyin Jini Domin su samu Gudana Yadda ya kamata. Hakan zai taimaka wajen rage Ciwon Hawan Jini da kuma Samar da Kariya ga wadanda basu da Cutar.

Ayaba tana Magance Dukkannin wata Matsala da ta Shafi Ciki. Sinadarin Faiba da take kunshe da shi kan taimaka wajen magance matsalolin Cushewar Ciki, Kumburin Ciki, Gudawa, Yawan Iska da sauran su.

Ayaba na da sinadari Kabohaidret wanda ke wadata Jikin Mutum da Kuzari. Amfani da Ayabar zai bada Kuzari da mutum ke bukata. Sannan Tana da Bitamin dake Taimakawa Lafiyar Kwakwalwa da Kuma Kara Kaifin Basira. Sinadarin Fotashiyom na bawa Tsoka ‘Karfi, da Gudanar da aiki yadda ya dace. Hakan ke Taimakawa Wajen Karawa Maza ‘Karfin Mu`amalar Aure. Har wa yau tana Sanya Saurin ‘Koshi.

Ayaba na kara Karfi ga masu Motsa Jiki Saboda Kuzari da take karawa Mutane.

Ayaba na dauke da sinadaran Antiokzidant wanda ke kare Mutuwar Kwayoyin Halittar Mutum. Wannan ya Sanya amfani da ita ke inganta lafiyar Jiki da na Fata. Sannan ta kan bada Kariya ga Dukkan Gabobin Jiki Dangane da Cututtuka da dama Harma da Cutar Daji. Tana Taimakawa Mata masu Juna Biyu Wajen Girma da kuma Lafiyar Kwakwalwa abin da ke Cikinta.

Amfani da Ayaba (Banana) da yawa a lokaci guda kan ingiza Ciwon Suga Saboda Sinadarin Suga Dake cikin. Ga Masu Ciwon Suga Amfani da Ayaba da yawa kan zamo musu Barazana.

Ga Masu Ciwon Koda, Lura da yanayin Amfani da ita na da Muhimmanci Saboda Sinadarin Fotashiyon na ciki zai iya Cutar da su.

Yabintu Abubakar

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos