Home ยป Amfanin Shan Madara

Muhimmancin Anfani da Madara ga Dan Adam na da yawa. Madara abune da ake anfani da shi tun fil azal a matsayin abinci da kuma magani.

Shan madara na da anfani wajen wadata jikin dan adam da Sinadarin Kalshiyom. Sinadarin Kalshiyom na Kara Karfin Kashi, Karin Jini da sauran su. Ba wannan kadai ba, Madara na Kunshe da Sinadarai da dama da ke da anfani a jiki.

Bincike ya nuna cewa, ana samun Sinadaran Bitamin, Minaral, Frotin, Antiokzidant da kuma lafiyayyan maiko a cikin ta. Dukkan wadannan sinadarai na taka muhimmiyar rawa wajen inganta lafiya da rayuwar dan adam.

Muhimmancin Anfani da Madara na nuna cewa anfani da shi a kullum kan taimaka wajen inganta garkuwan jikin mutum. Sinadaran Zink, Bitamin D, Bitamin A, da Frotin dake cikin ta na taimakawa lafiyar garkuwan jiki ta fannin kara karfin yakar cututtuka.

Masana lafiyar abinci sun bayyana cewar sinadarin Kalshiyom dake cikin madara na da anfani wajen inganta lafiyar Kashi, Ciwon Hakori, kare mutum daga cutar Rashin Kwarin Kashi. Ana Bukatar Mutane Sun Amfani Cukuyi, Yogot, Madaran `ya`yan itatuwa da dukkan nau`in madara da zai bada wannan sinadari da ake bukata.

Madara na da anfani wajen inganta lafiyar Zuciya, bincike ya nuna cewar wadan da ke anfani da madara a kullum ba su kamuwa da Cutukan Zuciya, Ciwon Suga ko Hawan Jini.

Haka zalika, anfani da madara na inganta lafiyar Gashi da Fatar Jiki. Sinadarin Zink da Bitamin A dake ciki zai Sanya samun fatar jiki ta Dinga sheki. Sannan Frotin dake ciki ya inganta lafiyar Gashi.

Shan madaran dabba da ba`a sSarrafa ta ba kai Tsaye na da hadari ga wadan da ke da Raunin Garkuwan jiki. Wadan da ke da wasu cututtuka kamar cuta mai karya Garkuwar Jiki (HIV), Tarin TB da sauran su. Likitoci na bada shawarar su Kaucewa shan danyar Madaran.

 

Yabintu Abubakar

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos