Home » An Bayyana Hanyoyin Kariya Daga Cutar Kansar Mama.

A ranar litinin 30th ga watan oktoba na Shekarar 2023 Ƙungiyar Anitomia ta Gudanar da bikin cikar kano 56 da kafuwa sannan tayi Amfani da wannan dama wajen wayar da kan Al’umma kan cutar kansar mama.

Dr Maryam Nasir Aliyu, ita ce shugabar sashen kula da lafiyar jiki ta jama’ar yusuf Maitama sule, Inda ta bayyana a Kafa watsa labarai, Yadda ake kamuwa da kansar da kuma yadda ake gane Alamomin cutar inda suka hada da jin wani kurji a mama ko mama daya yafi daya girma ko fitar da ruwa ko jini a jikin maman.

Sannan ta bayyana cewa wasu kwayoyin halitta acikin mama wanda ake kira cells sune idan suka mutu suke haifar da kansar mama inda ta bayyana matakan da za’abi dan magance kamuwa da cutar kansar Mama,

Matakan sune Kauracewa shan taba sigari, Shan shisha, da dai sauran su inda tayi karin bayani akan shan shisha “Shan shisha na awa daya dai dai yake da shan taba sigari sama da kara 100.

Rashin motsa jiki, da kiba mai maitsanani dan haka taja hankali akan ake motsa jiki, sai chemical da akesawa wajen nunar da abu.

Dr Maryam, taja hankalin mata da suke ziyartar Asibiti domin gwajin kansar mama lokaci zuwa lokaci.

Prof. Mukhtar Atiku Kurawa shugaban jama’ar yusuf maitama sule, Ya bayyana cewa makasudin taron shine sabida abubuwa guda biyu na daya kano ta cika shekara 56 da kafuwa da kuma bikin ranar kasan mama ta duniya.

Kazalika yace Ya kamata mata sun riqa gwajin kasar mama lokaci zuwa lokaci domin tabbatar da lafiyar su.

Suwaiba Abdullahi Sarki

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos