Home ยป Amosani Gaba (Ciwon Guiwa)

Amosanin Gaba Wato Arthritis a Turance. Ciwo ne da Ke Sanya Kunburi da Radadi ko Ciwon Gabar Ko Gababobi fiye da daya a Jikin Mutum.

Manyan Alamomin Amosanin Gaba Sune Radadi ko Ciwo da kuma Sarkewar Gabar mutum. Wadannan alamomi na Tsananta a lokain da shekarun mutum suka ja. Sauran sun hada da kumburi da kuma janza launin gabar tayi ja ko mutum ya kasa iya motsa ta.

Mafi yawan nau`inkan wannan cuta da ake fuskanta sune amosanin da ke sa sudewar mahadin gaban wanda ake kira Osteoarthritis a turance. Da kuma amosanin da ke Sanya kunburin gaba wato Rheumatoid arthritis. sannan anfi samunsu a gaba kamar irin guiwa.

Nau`in abincin da mutum ke ci na shafar lafiyar gabar sa. Hakan yasa wasu daga cikin sinadaran dake jikin dan adam ke haifar da cutar Amosanin Gaba.

Ciwo ko wasu larurori da mutum ke da shi kan sanya shi kamuwa da wannan cuta.

Wadannan Cututtukan sun hada da mummunan kiba ko teba, karanci ko yawan wasu sinadarai a jikin dan adam. Abubuwan da ke kara hadarin kamuwa da wannan cuta sun hada da tarihin cutar a dangi. sauran sune jinsin mutum, shekaru, kiba ko tsohuwar karaya.

Magance Amosanin gaba na nufin kawar da alamomin da cutar ta zo da shi kamar kumburin ko kuma radadi da sarkewar gabar.

Yabintu Abubakar

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos