Home » ALAMOMIN CUTAR HUHU

Ranar 12 ga watan Nuwamba ne ake bikin ranar cutar huhu ta duniya a kowace shekara da nufin wayar da kan jama’a game da cutar huhu, wadda daya che daga cikin Cututtukan da ke haddasa mutuwar kananan yara a duniya.

ALAMOMIN CIWON SUN HADA DA

  1. TARI: Mutumin da ke fama da ciwon huhu zai kasance yana fama da dadadden tari wanda kan iya zamowa mai hade da jini a wadansu lokutan.
  2. ZAZZABI: Wannan na iya kasancewa mai tsananin zafi ko kuma kadan kadan.
  3. CIWON ƘIRJI: Ciwon huhu na iya haifar da zafin kirji mai tsanani wanda ke daɗa muni yayin da kake numfashi ko tari.
  4. KARANCIN NUMFASHI: Masu cutar na iya samun wahalar numfashi ko kuma suna iya yin saurin numfashi fiye da yadda aka saba.
  5. GAJIYA: Haka kuma daga cikin alamun cutar akwai yawan gajiya, ko rashin kuzari.
  6. TASHIN ZUCIYA KO AMAI: A wasu lokutan wannan cuta na iya saka tsahin zuciya, musamman ga yara da tsofaffi.
  7. RUDANI: A cikin tsofaffi, rudani na iya zama alamar wannan cuta
  8. RASHIN CI ABINCI: Mutanen da ke fama da ciwon huhu na iya samun matsalar rashin son cin abinci.
  9. SAURIN BUGUN ZUCIYA: zuciyarka na iya bugawa da sauri fiye da Yadda ta saba saboda kamuwa da cutar.
  10. LEƁUNA MASU LAUNIN SHUƊI DA FARCE: A lokacin da cutar ta tsananta ta kan jawo sauyawar launin lebe da farata zuwa launin shudi-shudi saboda rashin iskar oxygen.

JAN HANKALI
Alamun ciwon huhu na iya zamowa mai sauƙi ko mai tsanani kuma yana iya zuwa ba zato ba tsammani ko kuma ta shige mutum da kadan-kadan. Duk wanda ke fuskantar waɗannan alamun ya kamata ya nemi kulawar likita cikin gaggawa.

Idan kuna zargin kuna da ciwon huhu, tuntuɓi mu a yau ba tare da wani bata lokaci ba.

Umar Abubakar Imam

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos